Nigerian Language Syllabus, Hausa Language scheme of work primary 6 Federal. Karatu Don Auna Fahimta– Schemeofwork.com
ZANGO NA FARKO DARASI; HAUSAN AJI SHIDA
MAKO 1
BATU/MAKASUDI: Tsarin Sassaukar Jimla:
- Ma’anar jimla a takaice
- Bada misalan jimloli
AYYUKA
- Malami: Ya kawo wasu misalan jimlolin a aji, tare da nuna wa dalibai sassan jimlolin.
MAKO 2
BATU/MAKASUDI: Tsarin Sassaukar Jimla:
- Bayani akan sashen suna
- Bayani akan sashen aikatau (bayani)
AYYUKA
- Malami: Ya bukaci dalibai suyi kokarin misalta kawo manufar sassaukar jimla, da kuma iya rarrabawa tsakanin sassauka da wadda ba sassauka ba, don duk inda suka gan susu iya bambance su cikin sauri.
MAKO 3
BATU/MAKASUDI: Kalmomi masu Ma’ana Daya:
- Ma’anar kalma
- Misalan kalmomi masu ma’ana daya
AYYUKA
- Malami: Tare da dalibai su kawo ire-iren wadannan kalmomi a cikin aji, tare da kawo ma’anoninsu.
MAKO 4
BATU/MAKASUDI: Kalmomi masu Ma’ana Daya:
- Ire-iren kalmomi masu ma’ana iri daya
- Jimloli (Kalmomi biyu kofiye da haka masu ma’ana iri daya)
AYYUKA
- Malami: Ya kawo wa ddalibai wasu kalmomin don su nemo ma’anonin su a rubuce a matsayin aikin gida.
- Sannan daga baya malami ya yi kokarin sa su gina jimloli ta hanyar yin amfani da wadannan kalmomi da wadannan kalmomi da suka nemo ma’anoninsu a cikin aji a aikace.
MAKO 5
BATU/MAKASUDI: Karatu Don Auna Fahimta:
- Ma’anar karatu domin fahimtawa
- Karanta labara
AYYUKA
- Malami: Ya samo wasu labarai daga wasu littatafai a karanta, a kuma yi bayanin tsauraran kalmomin cikin labaran, sannan a amsa tambayoyi.
MAKO 6
BATU/MAKASUDI: Karatu Don Auna Fahimta:
- Sababbin kalmomi cikin labara
- Furta sabobbin kalmomi
AYYUKA
- Malami tare dadalibai suyi kokarin fahimtar darasin da labarin yake Cauke dashi tare da nuna wa Calibai muhimmancin koyi da waCannan darussa ko kauce masu a rayuwa saboda illar da take tattare da su.
MAKO 7
BATU/MAKASUDI: Karatu Don Auna Fahimta:
- Muhimman kalmomi da ma’anarsu
- Tamboyoyi da aiki
AYYUKA
- Malami: Ya tsamo muhimman kalmomi don yiwa Calibai bayanin ma’anarsu.
MAKO 8
BATU/MAKASUDI: Ci Gaba Da Rubutun Wasika:
- Ma’anar wasika yar’gida
- Tsare-tsare akan rubutun wasika yar gida
AYYUKA
- Malami: Yayi wa Calibai bayani dalla- dalla kan matakan rubuta wasika ‘yar gida, da kuma kowane bangare da ta kunsa. Malami yaba wa yara aikin gida domin su rubuto wasika ‘yar gida.
MAKO 9
BATU/MAKASUDI: Rubutun Wasika:
- Ka’idojin Rubutun Wasikar Yar’gida
- Mutanen da Wasikar Yar’gida ta Shafa
AYYUKA
- Malami: Ya umarci Calibai da su fito gaban allo su rubuta yadda a ke tsara muhimman bangarorin wasika don sauran Calibai su gani a aikace, sannan ya fito masu dagyare-gyaren daya gani.
MAKO 10
BATU/MAKASUDI: Ci Gaba Da Rubutun Hannu:
- Manyan bakaken Hausa
- Kananan bakaken Hausa
AYYUKA
- Malami: Ya kara ba wa yara ayyukan da suka shafi rubutu.
MAKO 11
BATU/MAKASUDI: Ci Gaba Da Rubutun Hannu:
- Manyan tagwayen bakaken Hausa
- Kananan tagwayen bakaken Hausa
AYYUKA
- Malami: Ya duba rubuce-rubucen da Calibai sukayi, tare da yi masu gyara a wuraren da sukayi kuskure.
MAKO 12
BATU/MAKASUDI: Ci Gaba Da Rubutun Hannu:
- Manyan da kananan wasulan Hausa
- Manya da kananan wasula masu goyo
AYYUKA
- Malami: Ya gwada wa Calibai yadda ake rubutu a allo da ma yadda ake rike fensiri a yayin rubutu
MAKO 13
Bitar Ayyukan baya
MAKO 14
Jarabawa
ZANGO NA BIYU DARASI; HAUSAN AJI SHIDA
MAKO 1
BATU/MAKASUDI: Karatun Gajerun Wasanni Kwaikwayo:
- Ma’anar Wasan Kwaikwayo
- Misalan Wasan Kwaikwayo
AYYUKA
- Malami: Ya yi kokarin kawo wa dalibai wasu wasannin kwaikwayo na dandali na mata da na maza, domin su gabatar a aji.
- Malami ya dubi littafin ‘Wasannin Yara’na Umaru Dembo ko wasu litattafan.
MAKO 2
BATU/MAKASUDI: Karatun Gajerun Wasanni Kwaikwayo:
- Bayyana Al’adun Hausawa da ake misalatawa a wasan kwaikwayo
- Muhimman darussa da wasan kwaikwayo ke dauke da su
AYYUKA
- Malami: Ya karanta wa yara wani rubutaccen wasan kwaikwayo, kamar’Uwar Gulma’ na Alhaji Muhammed Sada
MAKO 3
BATU/MAKASUDI: Karantun Gajerun Wasannin Kwaikwayo:
- Wasan Gyara Kayanka
- Wasan Langa
AYYUKA
- Malami: Ya jagoranci karanta su a aji tare da dalibai da kokarin bayyana darasin da suke koyarwa
MAKO 4
BATU/MAKASUDI: Karatun Rubutattun Wakoki:
- Ma’anar rubutacciyar waka
- Misalin rubutacciyar waka mai take ‘Mu je neman ilmu’
AYYUKA
- Malami: Ya sa yara su rera wannan wakar sannan a kawo masu wani littafi mai dauke da gajerun wakoki. Haka kuma, malami ya yi masu bayanin yadda fadakarwar dake cikin wakokin za ta amfane su a rayuwarsu ta yau da kullum
MAKO 5
BATU/MAKASUDI: Karatun Rubutacciyar Waka:
- Bayanin Baiti Rubutacciyar wakar
AYYUKA
- Malami: Ya yi bayanin yadda zubi da tsarin wakar yake ga dalibai.
MAKO 6
BATU/MAKASUDI: Karatun Rubutacciyar Waka:
- Fitar da Kebabbun da ke cikin
- Ma’anar Kebabbun Kalmomin
AYYUKA
- Malami: ya yi bayanin wadansu abubuwa na daban da wakar ta tabo
MAKO 7
BATU/MAKASUDI: Dabarun Tafiyar da Ruyuwa:
- Ma’anar Dabarun Tafiyar da Rayuwa
- Matakan Tsara Rayuwa
AYYUKA
- Malami: Ya kara kawo jerin wasu dabarun tafiyar da rayuwa, tare da tattauna su da dalibai.
MAKO 8
BATU/MAKASUDI: Dabarun Tafiyar da Rayuwa:
- Bambance-bambance da ke cikin matakan tsara rayuwa tsakanin namiji da kuma mace
- Bayanin tanade-tanaden da ke cikin dabaruntafiyar da rayuwa
AYYUKA
- Malami: Ya ba wa dalibai damar kawo nasu dabarun tafiyar da rayuwa da suka sani da kuma yadda zasu dabbaka dabarun a rayuwarsu
MAKO 9
BATU/MAKASUDI: Shan Miyagun Kwayoyi:
- Ma’anar Miyagun Kwayoyi
- Misalan Miyagun Kwayoyi
AYYUKA
- Malami: Ya jaddada wadalibai illolin shan miyagun kwayoyi da kawo misalan irin mutanen da suka lalace saboda shan miyagun kwayoyi
MAKO 10
BATU/MAKASUDI: Shan Miyagun Kwayoyi:
- Illolin Shan Miyagun Kwayoyi
- Bayanin Muhimman Kalmomi
AYYUKA
- Malami: Ya yi bayani a kan irin asarar da kasa tare da iyayen masu shan kwayoyi ke yi
MAKO 11
Bitar Ayyukan baya
MAKO 12
Jarabawa
Nigerian Language Syllabus, Hausa Language scheme of work primary 6 Federal. Karatu Don Auna Fahimta– Schemeofwork.com
ZANGO NA UKU DARASI; HAUSAN AJI SHIDA
MAKO 1
BATU/MAKASUDI: Wasanin Dandali:
- Bayanin Wasanin Dandali
- Tantance Wasanin Dandali
AYYUKA
- Malami: Ya jagoranci cfalibai su aiwatar da wani wasan dandali acikin aji ko a wajen aji
MAKO 2
BATU/MAKASUDI: Wasanin Dandali:
- Misalan Wasanin Dandali
- Fito da fa’idojin wasanin dandali
AYYUKA
- Malami: Ya dubi littafin Wasanin Rara na Umaru Dembo
MAKO 3
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sadarwa:
- Ma’anar Sardawa
- Ire-iren Hanyoyin Sadarwa
AYYUKA
- Malami: Ya jagoranci cfalibai su yi bayani akan allo game da darasin da malami ya rubuto
MAKO 4
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sadarwa:
- Hanyoyin Sadarwa na Zamani
- Hanyoyin Sadarwa na Gargajiya
AYYUKA
- Malami: Ya bayyana abin da hanyoyin sadarwa na zamani da na gargajiya suka kunsa.
MAKO 5
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sadarwa:
- Gidan Waya
- Gidan Waya da/Wasika
AYYUKA
- Malami: Ya kara tsefe bayanin kan rukunonin hanyoyin sadarwa
MAKO 6
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sadarwa:
- Sabuwar fasaha/Sadarwa
- Ire-iren Hanyoyin Sadarwa na Zamani dana Gagajiya
AYYUKA
- Malami: Ya kawo sunayen hanyoyin sadarwa na karta-kwana ko sha-yanzu magani-yanzu
MAKO 7
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sufuri:
- Ma’anar Sufuri
- Lissafa Hanyoyin Sufuri iri-iri
AYYUKA
- Malami: Ya kara yi wa Calibai cikakken bayani a kan hanyoyin sufuri.
MAKO 8
BATU/MAKASUDI: Hanyoyin Sufuri:
- Kawo Amfanin Hanyoyin Sufuri
- Hanyoyin Sufuri na Gargajiya dana Zamani
AYYUKA
- Malami ya yi kokarin kai Calibai ziyara zuwa filin jirgin sama da tashar jirgin kasa idan akwai
MAKO 9
BATU/MAKASUDI: Bukukuwan Hausawa:
- Ma’anar Bikin Sallah
- Bayanin Bikin Sallah
AYYUKA
- Malami: Ya sa Calibai su bayar da labarin wani bikin sallah da suka taba halarta
MAKO 10
BATU/MAKASUDI: Bukukuwan Hausawa:
- Bayanin Bikin Mauludi
- Muhimmancin Bukukuwan Sallah
AYYUKA
- Malami: Ya sa Calibai suyi bayanin yadda ake hawan sallah a matsayin aikin gida
MAKO 11
BATU/MAKASUDI: Kwalliya da Tufafin Hausawa:
- Bayanin zane da kwalliya da ban daban
- Bayanin zanen kwalliya da tufafi
AYYUKA
- Malami: Ya jagoran ci Calibai da sununa yanda ake ado da kuma kwalliya.
- Malami: Ya fito daCalibai don su kwatanta yadda ake kwalliya
MAKO 12
Maimaitacin Aikin Baya
MAKO 13
Jarabawa