Nigerian Language Syllabus, Hausa Language scheme of work primary 5 Federal, tambayoyi, Ƙa’idojin Rubutu, Schemeofwork.com
FIRST TERM HAUSA LANGUAGE SCHEME OF WORK FOR PRIMARY FIVE
NIGERIAN LANGUAGE (NL)
HAUSA LANGUAGE PRIMARY FIVE AJI BIU ZANGO NA DAYA FIRST TERM
MAKO: Na daya (1)
BATU/MAKASUDI
Kidaya:
i. AlRaluman Kidaya: Dari da daya zuwa dari da hamsin (101 – 150)
AYYUKA
Malami: Ya yi RoRarin nunawa dalibai wadannan alRaluman Ridaya ta hanyar amfani da duwatsu ko wasu abubuwan daban. Malami ya nuna wa dalibai yadda ake tara adadi da debewa.
MAKO: Na biyu (2)
BATU/MAKASUDI
Auna Fahimta:
i. Ma’anar labari
ii. Karanta labari
AYYUKA
Malami: Ya samo jawabai da labarai daban-daban, makamanta wadanda aka kawo a sama, don auna fahimtar dalibai.
MAKO : Na uku (3)
BATU/MAKASUDI
Muhimmancin Labari:
ii. Karanta labari a zuci
AYYUKA
Malami: Ya taimakawa dalibai, wajen fito
da muhimman kalmomi tare da yi masu bayanin wadannan kalmomi.
MAKO: Na hudu (4)
BATU/MAKASUDI
Saukakan Jimloli:
i. Ma’anar jimla
ii. Ma’anar sassauRar jimla
AYYUKA
Malami: Ya bawa ɗalibai aikin gida, domin su rubuto sauƙaƙan jimloli masu ɗauke da
bayani da kuma masu ɗauke da tambaya.
MAKO: Na biyar (5)
BATU/MAKASUDI
Sauye-sauyen Kalma:
i. Gina kalma
ii. Ci gaba da gina kalma
AYYUKA
Malami: Ya kawo misalan kalmomi, da yadda ake samun sauye-sauye a cikinsu.
Malami: Ya sa ɗalibai su yi ta sauya kalmomi
MAKO: Na shida (6)
BATU/MAKASUDI
Karatu don Auna Fahimta
i. Ma’anar labara
ii. Karanta labara da kansu
AYYUKA
Malami: Ya gayyato wani jami’in kula da lafiya don bayyana wa ɗalibai hanyoyin kamuwa da sarke-haƙora, da kuma hanyoyin riga-kafin kamuwa do ita.
Malami: Ya yi bayani kamar yadda ya
Dalibai: A ba su labari su karanta da kansu su kuma amsa tambayoyi
gabata a bya.
Ɗalibai: A yi masu tambayoyi su amsa
MAKO: Na bakwai (7)
BATU/MAKASUDI
Karatu don Auna Fahimta:
i. Kawo labara da suka karantan
AYYUKA
Malami: Ya kamar yadda bayani ya gabata
Ɗalibai: A ba su labari su karanta da kansu su kuma amsa tambayoyi
MAKO: Na takwas (8)
BATU/MAKASUDI
Karatu don Auna Fahimta:
i. Kawo muhimmancin kalmomin cikin labara
ii. Karanta labara a zuci
AYYUKA
Malami: Ya yi ƙoƙarin kawo jimloli da kuma jawabi waɗanda ba a bi ƙa’idojin rubutu ba domin ɗalibai su rubuta su daidai.
MAKO: Na tara (9)
BATU/MAKASUDI
Ƙa’idojin Rubutu:
i. Kiyaye ka’idojin rubutu
ii. Kawo wasali
AYYUKA
Malami: Ya fayyacewa ɗalibai kowace alama da muhallun amfaninta
MAKO: Na goma (10)
BATU/MAKASUDI
Ƙa’idojin Rubutu:
i. Kayi amfani da aya
ii. Tantance jimla
AYYUKA
Malami: Ya sa ɗalibai su rubuta tunaninsu ta hanyar kallon abin da ke faruwa a wanan hoto daban, ko abin da ke faruwa a kewaye da su
MAKO Na sha ɗaya (11)
BATU/MAKASUDI
Ci gaba da Rubutun Hannu:
i. Rubuta baƙeƙe da wasula a allo
ii. Bayyaba tunaninsu ta hanyar rubutu
AYYUKA
Malami: Ya sake maimaita abin da aka yi a sama tare da ba ɗalibai aikin gida
Bitar aikin baya
MAKO: Na sha biyu (12)
BATU/MAKASUDI
Ci gaba da Rubutun Hannu:
i. Rubuta baƙeƙe da wasula
ii. Rubuta tubabu a littafi
AYYUKA
Jarabawa
MAKO : Na sha uku (13)
BATU/MAKASUDI
Bita Ayyukan Baya
AYYUKA
MAKO : Na sha hudu (14)
BATU/MAKASUDI
Jarabawa
Nigerian Language Syllabus, Hausa Language scheme of work primary 5 Federal, tambayoyi, Ƙa’idojin Rubutu, Schemeofwork.com
SECOND TERM HAUSA LANGUAGE SCHEME OF WORK FOR PRIMARY FIVE
NIGERIAN LANGUAGE (NL)
HAUSA LANGUAGE PRIMARY FIVE
ZANGO NA BIYU
DARASI: HAUSA
AJI BIYAR
MAKO: Na daya (1)
BATU/MAKASUDI
Gajeren Rubutaccen
Wasan kwaikwayo:
i. Bayyana jigon wasan kwaikwayo
ii. Jera manya da kananan ‘yan wasa
AYYUKA
Malami: Ya sa ɗalibai su karanta dukkan littafin Wasan Mafara, sannan su
kwantanta yinsa a aikace.
MAKO: Na biyu (2)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Rubutaccen Wasan kwaikwayo:
i. Wasan mafara
ii. Uwar Gulma
AYYUKA
Malami: Ya sa ɗalibai kawo misalan wasu littatafan makamantan waɗannan.
MAKO : Na uku (3)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Waƙoƙi:
i. Ma’anar waƙa
ii. Karanta waƙa
AYYUKA
Malami: Ya ƙara kawo wata gajeriyar rubutacciyar waƙa. Ya rera wa ɗalibai. Ya fito da muhimman kalmomin cikin waƙa, tare da faɗa masu ma’anoninsu.
MAKO: Na hudu (4)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Waƙoƙi:
i. Rera Waƙoƙi
ii. Mahimmancin kalmomin da ke cikin waƙa
AYYUKA
Malami tare da ɗalibai su yi ƙoƙarin
tsamo sabbin kalmomi don tsattsefe su
MAKO: Na biyar (5)
BATU/MAKASUDI
Adon Magana:
i. Ma’anar adon magana
ii. Bada bayanin adon magana
AYYUKA
Malami: Ya jagoranci dalibai wajen bayyana musu ma’anonin waddanan adon magana, sannan yasa yara su kawo wa dandansuka sani don tattannawa a aji
MAKO : Na shida (6)
BATU/MAKASUDI
Gabatar da Karya Harshe:
i. Kawo yadda ake karya harshe
ii. Hanyoyi karya harshe
AYYUKA
Malami: Ya misalta yin gagara-gwari da ingiza-bami ta hanyar kawo misali don
ɗalibai su fahimta. Sannnan ya umarci ɗalibai, su ma su kawo misalai tare da aiwatar da su a aji.
MAKO: Na bakwai (7)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Labarai:
i. Bayar da labarin gargajiya
ii. Labaran gargajiya
AYYUKA
Malami: Ya sa ɗalibai su kawo wani gajeren labari ko tatsuniya, tare da fito
da muhimman kalmomin cikin labarin
MAKO: Na takwas (8)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Labarai:
i. Fito da darassan labaran gargajiya
ii. Labaran gargajiya
AYYUKA
Malami: Ya tsamo irin darussan da su ke cikin labarin.
MAKO: Na tara (9)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Labarai:
i. Fito da bayanai daga labaran gargajiya
ii. Misalan labarun gargajiya
AYYUKA
Malami: Ya zayyana irin muhimmancin da
labarun gargajiya ga al’ummar Hausawa
MAKO: Na goma (10)
BATU/MAKASUDI
Gajerun Labarai:
i. Muhimmancin labaran gargajiya
ii. Muhimmancin kalmomin cikin labaran gargajiya
AYYUKA
Malami: Ya zayyana irin muhimmancin da
labarun gargajiya ga al’ummar Hausawa
MAKO: Na sha daya (11)
BATU/MAKASUDI
Bita Ayyukan Baya
MAKO : Na sha biyu (12)
BATU/MAKASUDI
Jarabawa
Nigerian Language Syllabus, Hausa Language scheme of work primary 5 Federal, tambayoyi, Ƙa’idojin Rubutu, Schemeofwork.com
THIRD TERM HAUSA LANGUAGE SCHEME OF WORK FOR PRIMARY FIVE
NIGERIAN LANGUAGE (NL)
HAUSA LANGUAGE PRIMARY FIVE
ZANGO NA BIYU
DARASI: HAUSA
AJI BIYAR
MAKO: Na daya (1)
BATU/MAKASUDI
Tsaftar Jiki:
i. Ma’anar tsaftar
ii. Misalan sassan jiki
AYYUKA
Malami: Ya tsara kwatanta wa ɗalibai yadda ake tsaftace tufafi da irin
muhimmancin da yake tattare da tsaftace su da illar rashin tsaftace su da kuma zama da kazanta
MAKO: Na biyu (2)
BATU/MAKASUDI
Tsaftar Jiki:
i. Bayyanin yadda ake tsaftace sassan jiki
ii. Hanyoyin tsaftace jiki
AYYUKA
Malami: Idan zai yiwu, ya samo jami’in kiwon lafiya don ya ƙarawa ɗalibai bayanin muhimmancin tsafta
MAKO: Na uku (3)
BATU/MAKASUDI
Sunayen Hausawa:
i. Kawo sunayen hausawa
ii. Tantance sunayen yanka da na rana da na yanayi
AYYUKA
Malami: Ya ƙara bayyana wa ɗalibai muhimmancin sunaye ya kuma umarce su da su rubutu sunayen danginsu, ta hanyar ba su aikin gida
MAKO : Na hudu (4)
BATU/MAKASUDI
Sunayen Hausawa:
i. Bayani sunan yanka
ii. Bayanin sunan rana
ii. Muhimmancin sunayen
AYYUKA
Malami: Ya bambanta tsakanin
sunayen yanka, gargajiya da na rana
Ɗalibai: Su rubuto sunayen rana guda biyar
MAKO: Na biyar (5)
BATU/MAKASUDI
Tsarin saurautun Hausawa:
i. Ma’anar sarauta Hausawa da tsarinta
ii. Bayanin nadin sarauta
AYYUKA
Malami: Ya sa ɗalibai su misalta yadda ake naɗin sarauta a cikin aji. Ya kuma shirya kai ziyarta tare da ɗalibai don halartar wani taro na naɗin sarauta
MAKO: Na shida (6)
BATU/MAKASUDI
Tsarin sarautun Hausawa:
i. Tantance sunayen sarauta da ayyukansu a ƙasar Hausa
ii. Misalan nadin sarauta
AYYUKA
Malami: Ya shirya ziyara zuwa gidan sarki tare da ɗalibai don ganin yanayin
zaman fada.
MAKO Na bakwai (7)
BATU/MAKASUDI
Sana’o’i:
i. Ma’anar sana’a
ii. Bada bayanin sana’a
iii. Muhimmancin sana’o’in Hausawa
AYYUKA
Malami: Ya kara fayyacewa ɗalibai yadda ake aiwatar da waɗannan sana’o’in.
Ɗalibai: Su rubuto sana’o’in mata guda biyar
MAKO : Na takwas (8)
BATU/MAKASUDI
Sana’o’i:
i. Sana’oi noma da ƙira
ii. Yadda ake aiwatar da noma da ƙira d. s.
AYYUKA
Malami: Ya gayyato masu aiwatar da waɗannan sana’o’in don ƙara fayyacewa ɗalibai yadda ake yinsu
MAKO: Na tara (9)
BATU/MAKASUDI
Kayan sana’a:
i. Ma’anar kayan sana’a
ii. Misalan kayan sana’a
AYYUKA
Malami: Ya kai yara wuraren da ake aiwatar da waɗannan sana’o’in domin su gani da ido
MAKO: Na goma (10)
BATU/MAKASUDI
Bikin suna:
i. Ma’anar biki
ii. Bayanin yadda ake gudanar da bikin suna
AYYUKA
Malami: Ya bai wa ɗalibai aikin gida, domin kawo ya rubuto yadda ake bikin suna a garinsu, sannan su tattauna irin bambance- bambacen da ke akwai a aji
MAKO: Na sha daya (11)
BATU/MAKASUDI
Bikin suna:
i. Misalan bikin suna
ii. Muhimmancin da ilolin bikin suna
AYYUKA
Malami: Ya bayyanawa ɗalibai irin nishaɗin da tattare da bikin suna
Ɗalibai: Su kawo irin ilolin da suke na tattare da bikin suna
MAKO: Na sha biyu (12)
BATU/MAKASUDI
Maimaicin Ayyukan Baya
MAKO: Na sha uku (13)
BATU/MAKASUDI
Jarabawa