Senior Secondary Humanities Curriculum Federal. SS 2 Hausa Language Scheme of Work. Malami ya yiwa –Schemeofwork
HAUSA LANGUAGE SS2 FIRST TERM
ZANGO NA DAYA AJI BIYU
MAKO | JIGO/MAKASUDI | AYYUKA |
1 | Azuzuwa Kalmomi: Malami ya koyar da ma’anar kalma. Sannan ɗalibai su iya tantace azuzuwan kalmomi, kamar:- Suna da rabe-rebansaWakilin suna – ire-irensaSifa – da abin da ta ƙunsa | |
2 | Azuzuwan Kalmomi: A cigaba da koyar a azuzuwan kalmomi irin su:- AikatauBayanauNunau | |
3 | Azuzuwan Kalmomi: Malami ya ƙarƙare koyar da azuzuwan kalmomi kamar su;- MafayyacMa’auni tare da dimbin misalai a cikin jimla. | |
4 | Nazarin Waƙoƙin Baka: Malami ya yiwa ɗalibai bitar ma’anar waƙoƙin baka. Manufofin da muhimmacin waƙoƙin msl: Wayar da kai., Zambo, zuga, nishaɗi, habaici, yabo, raha, kewa. | |
5 | Nazarin Waƙoƙin Baka: Malami ya koyar da ire-iren waƙoƙin baka msl: waka aurenikadakalugude | |
6 | Ginin Kalmomi: Malami zai koyar da: Ma’anar ginin kalma, kamar saiwa ko tushen kalma ds. | |
7 | Ginin Kalma: Malami zai koyar da: abubuwan da kalma ta Ƙumsa kamar, ɗafi, ɗafa-goshi, ɗafa-ciki da ɗafa-ƙeya. | |
8 | Insha’I: Malami zai karantar da; wasiƙu bisa tsari da sigoginsu da ƙa,idojin rubutu | |
9 | Nazarin Tatsunniyoyi da Labarai: Malami zai koyar da nazarin tatsuniyoyin da labarai masu koyon dabarun zaman duniya. | |
10 | Nazarin Tatsunniyoyi da labarai: Malami zai koyar da: kyawawan halaye da munanan halaye da ake samu daga tatsuniyoyi da labarai. | |
11 | Camfe-camfe da magugunan gargajiya: Malami zai koyar da: iren-iren camfe-camfen Hausawa; da ma’anarsu da ma’anar magungunan gargajiya da ire-iren magungunan gargajiya, masu bada su da muhimmancinsu. | |
12 | Maimaitawa | |
13 | Jarabawa |
FCT Senior Secondary Humanities Curriculum . SS2 Hausa Language Scheme of Work Federal. –Schemeofwork
HAUSA LANGUAGE SS2 SECOND TERM
ZANGO NA BIYU AJI BIYU
MAKO | JIGO/MAKASUDI | AYYUKA |
1 | Nazarin littafin zube: Malami zai karantar da nazarin littafin zube ta fannin: Jigon littafi jaruntasoyayyabantausayigyaran hali dadubarun zaman duniya | |
2 | Ci gaba da nazarin littafin zube: Malami ya karantar da salon sarrafa harshe irinsu: babi – babitsara jimlolisakin layidubarun jan hankaliAmfani da kalmomi ds | |
3 | Furucin baƙaƙe da wasula: Malami zai koyar da: ma’anar tsarin sauti kamar: adadin baƙaƙe, misalisaukaka – B, C, D, F, dsadadin masu goyo, misalin: gy, gw, ts, sh, ds.adadin wasula tilo masu aure | |
4 | Ci gaba da furicin baƙaƙe wasula: Malami zai koyar da; furicin baƙaƙe; gurbin furiciyanayin furicimatsayin maƙwallato kamar mai ziza da marar ziza.furicin wasulla – tsayi, siga da tagwan wasali. | |
5 | Ci gaba da furucin baƙaƙe wasulla: Malami zai yi bitar ma’anar gaɓa. Tsarin baƙi, wasali (BW)Tsarin baƙi wasali, baƙi. (BWB)Tsarin baƙi wasali wasali (BWW)Rufaffiyar gaɓaBudaddiyar gaɓa ds. | |
6 | Nazarin littafin karin magana: Malami zai karantar da: Ma’anar Karin MaganaYadda ake Karin MaganaIre-iren Karin Magana | |
7 | Lokuta: Malami zai karantar da: ma’anar lokaciire-iren lokuta, kamarshuɗaɗɗen lokaci (i)shuɗaɗɗen lokaci (ii)lokaci sabaulokaci mai ci (i)lokaci mai ci (ii) | |
8 | Nazarin litaffin wasan kwaikwayo: Malami zai koyar da: Ma’anar wasan kwaikwayoJigo da zubi da tsari da sarrafa harshe ds. | |
9 | Ci gaba da nazarin littafin wasan kwaikwayo: Malami zai koyar da: Wuraren da ake wasan kwaikwayo. Misali rediyo, telebijin, dandali ds. | |
10 | Tunanin Bahaushe akan fatalwa: Malami zai koyar da: ma’anar fatalwa, yadda bahaushe ya fahimci fatalwa, kamar labaru game da fatalwamutuwakurwakishibege ds | |
11 | Maimaitawa | |
12 | Jarabawa |
FCT Senior Secondary Humanities Curriculum . SS2 Hausa Language Scheme of Work Federal. –Schemeofwork
HAUSA LANGUAGE SS2 THIRD TERM
ZANGO NA UKU AJI BIYU
MAKO | JIGO/MAKASUDI | AYYUKA |
1 | Auna fahimta: Malami zai yi bitar; Ma’anar auna fahimta, watau tabbatar da gane abubuwa da ake koyawa dalibai a lokaci guda domin a kaifafa fahimtarsu.Iya sanin ma’anar kalmomin Hausa | |
2 | Ci gaba da auna fahimta: Malami zai koyar da; Ire-iren auna fahimta:Na labari Na jawabi daNa waƙa ds. | |
3 | Ire-iren fassara: Malami zai koyar da; ire-iren fassara kamar; fassarar baƙi da baƙifassarar nan takefassara mai yanci | |
4 | Ci gaba da ire-iren fassara: Malami zai koyar da; rukunan fassara kamarnaƙaltaharsuna biyu danaƙaltar al’adu. Sannan ɗalibai zasu san; matakan fassara kamar;daidaituwar saƙo, da banbancin karin harshe. | |
5 | Nazarin littafin rubutacciyar waƙa: Malami zai koyar da; Nazarin waƙoƙi dangane da; jigozubi da tsarin baitoci | |
6 | Ci gaba da nazarin littafin rubutacciyar waka: Malami zai koyar da; salo da sarrafa harshe, kamar dabarun jawo hankali;amfani da ararrun kalmomi ds. | |
7 | Sana’oin gargajiya: Malami zai koyar da; ma’anar sana’oin gargajiya kamar,su, fawa, kaɗi, kitso,farauta, dori, gini, jima,da rini ds. | |
8 | Ci gaba da sana’oin gargajiya: Malami zai koyar da; Ire-iren kayan aikin sana’o’i gargajiyaƊalibai su san masu sana’o’i gargajiya | |
9 | Tunanin bahaushe akan iskoki: Malami zai koyar da; ma’anar iskoki,yadda Bahaushe ya fahimci iskoki, kamar masu;ban tsoro, baƙaƙen iskoki ko fararen iskoki | |
10 | Ci gaba da tunanin Bahaushe akan iskoki: Malami zai koyar da; Muhallinsu: kamar; tsamiya, faƙo, kuka, kogo, suri, gwalalo, juji da bayi ds | |
11 | Maimaitawa | |
12 | Jarabawa | |
13 | Jarabawa |