Hausa Language Scheme of Work for SS 1 Federal

7 Min Read
Schemeofwork.com
Scheme of Work

FCT Senior Secondary Humanity Syllabus. Federal Hausa Language Scheme of Work for SS 1. Rubutaccen Adabi Schemeofwork

HAUSA LANGUAGE SS1 FIRST TERM
ZANGO NA DAYA AJI DAYA

MAKOJIGO/MAKASUDIAYYUKA
1Ƙa’idojin Rubutu: A sanar da ɗalibai ma’anar ƙa’idojin rubutu .A koyar da darasi kan rabawa da haɗa kalmomi msl: Ali ne, Motar baƘa ce, ya ci, ds.Koyar da haɗa kalmomi. Msl’’ saboda’, ba ‘’sabo da’’ ba, ds.  
2Ci gaba da ƙa’idojin rubutu                      Gajeruwar mallaka- misali ‘’rigarsa’’ ba ‘’rigar sa’’ ba ‘’gidanmu’’ ba ‘’gidan mu ba’’. A koyar da ɗaurin /m/ ko /n/ da baƙaƙe masu goyo. Msl/m/ ”tambaya’’ ba ‘’tanbaya’’ ba./n/ za a yi ɗauri duk wuraren da baƙaƙe /b/, /m/ da /f/ ba su zo cikin kalma ba. Msl: /tinya/, ba timya ba. Ds.Ɗaurin baƙaƙe masu goyo msl: gyaggyora, shasshare, fyaffyace ds.     
3Sassan jimla:       i.  Ɗalibai su san ma’anar jimla       ii.  A koyar da sassan jimla.       a.  Yankin suna.       b.  Yanki aikatau 
4Fayyace abubuwa da ke sashen suna da aikatu: Yankin sunaSuna Amsa KamaW/SunaSifaMafayyaciMa’auniNunauYankin aikatauLamirin sunaManunin lokaciKarɓauBayanauAmsa kamaAikatau 
5Insha’i: Ya kasance ɗalibai sun iya Fadar ma’anar insha’iIre-iren insha’i msi:LabariSiffantawaMuhawaraTattaaunawaFayyacewaRubutun wasiƙa 
6Fadar ire-iren sigar insha’i: -Siffoffin insha’i GabatarwaGundarin labariKammalawa -A san matakan fitar da siffofin insha’i. Jeranta tunaniKyawun saloAmfani da kalmomi inda suka dace Amfani da gajerun jimloli Sakin layiDasa aya ko wakafi inda ya daceƘa’idojin rubutu 
7Rabe-rabe adabin baka:    Koyar da ma’anar adabin baka dangane da sigoginsu. Misali. Zobe:  –    Tatsuniya AlmaraHikayaLabarai ds. A duba Rebe-raben Adabi Da Muhimmancinsa, Na Dangambo A. Aimana Publishers. 
8Ci gaba da Adabin Baka:  A koyar da waƙoƙin makaɗa: Makaɗan Fada (Sarkin Taushin  S/Katsina)Makaɗan Jama’a (Mamman Shata)Makaɗan Sana’a (Illori Kalgo)Makaɗan Maza (Gambu (Wakan barayi) 
9Nazari Zobe:     Ɗalibai su iya karantawa da nazarin littafin Ƙagaggen labari (Zobe) ta gano JigoSaloSalon sarrafe harshe ds. 
10Malami ya koyar da: Bayanin salon sarrafa harshe Amfani da kalmomiDabarun jawo hankaliSakin layiBabi-babiTsara jimloli 
11Muhimmancin adabin baka wajen gane tarihin al’umma:   Malami ya sanar da ɗalibai tarihin kafuwar al’ummar Hausawa ta hanyar Adabin baka Kafuwar garuruwan Kano, da Barbushe, Tsumburbura.Durɓi ta kusheyiBayajida, kafuwar Hausa Bakwai da Banza Bakwai   
12Jihadin Shehu Danfodio:  Ɗalibai su sani da Bawa JangwarzoZuwan TurawaYaƙe-yaƙen Sarakunan Hausawa 
13MaimaitawaMaimaitawa
14JarabawaJarabawa

FCT Senior Secondary Humanity Syllabus. Federal Hausa Language Scheme of Work for SS 1. Rubutaccen Adabi Schemeofwork

HAUSA LANGUAGE SS1 SECOND TERM
ZANGO NA BIYU AJI DAYA

MAKOJIGO/MAKASUDIAYYUKA
1Ire-iren jimloli: A tabbata ɗalibai sun iya tantance ire-iren jimloli. Msl Jimla mai aikatauBala ya ci tuwoBinta ta sha ruwa ds.Jimla marar aikatauAkwai ruwaBabu tuwo ds. 
2Rabe rabe Rubutaccen Adabi: Malami ya koyar da ɗalibai. Ma’anar/rubutaccen adabiDa rabe-rabensa; kamarAdabin zamani (rubutacce)Abin lura wajen rarraba shi 
3Ci gaba:  Abubuwa da ake maida hankali Wajen rarraba rubutaccen AdabiTarihin shigowar Ajami da na BokoManufofin rubuce-rubuceZubi da tsarinsa. 
4Ci gaba:   Rubutattun waƙoƙin: ƙarni na 19ƙarni na 20Zube (ƙagaggen labari)Wasan ƙwaikwayo -Na talbijin            -Na radiyo            -Na dandamali 
5Nazarin littafin rubutacciyar waƙa:    Malami ya koyar da yadda ɗalibai za su gane saƙon da waƙa ta ƙumsa, kamar su ZubiTsariSaloJigo 
6Zubi da tsari:  A koyar da waɗannan: Tsarin baitoci – Ƙwar-biyu, ukuYawan baitociBuɗewa da rufewaSalon sarrafa harshe aron kalmomi, dabarar jan hankali 
7Abubuwan tarihi a Adabin baka; Ɗalibai su iya fito da abubuwan tarihi daga Adabin baka. Ire-iren Adabi baka da ya kunshiWaƙoƙin mataWaƙoƙin makaɗaTarihin (Yadda mutuwa ta zo) 
8 Ci gaba: Wasanni tsakanin ƙabiluWasanni tsakanin garuruwaSara ds. 
9Wasa ƙwaƙwalwa:   Yara su san Ma’anar wasa  ƙwaƙwalwaIre-iren wasa ƙwaƙwalwa 
10A koyar da: Hikimomin wasa ƙwaƙwalwa 
11MaimaitawaMaimaitawa
12JarabawaJarabawa

HAUSA LANGUAGE SS1 THIRD TERM
ZANGO NA UKU     AJI DAYA

MAKOJIGO/MAKASUDIAYYUKA
1Nazarin littafin wasan kwaikwayo: A koyawa ɗalibai ma’anar wasan kwaikwayo, da rubutaccen wasan kwaikwayo, dangane da la’akari da: Jigo Wayar da kaiGyaran haliNasihaNishadi 
2Ci gaba da nazarin: Malami ya koyar da ɗalibai so littafin wasan kwaikwayo kamar: Zubi da tsarin wasaKashiFitowaMaganar ɗan wasaSakin layi 
3Ci gaba da nazarin:    Ɗalibai su iya laƙantar littafin wasan kwaikwayo: Sarrafa harsheDacewar MaganaYin maganar KurmaYin maganar DandauduYin maganar Mata ds   
4Zamantakewar al’ummar Hausawa: Ya kasance malami ya koyar da Matsayi da ƙimar HausawaYadda Hausawa suka karkasa kansuFahimci ɗabi’u da aikin ko wane rukuniMa’anar zamantakewaRukunin jama’a da shekaru: yara, matasa, manya, ds. 
5Ci gaba da zamantakewar al’umar Hausawa: Fayyace ko wanne rukuni da aikinsa msl: Yara, Reno, aikin gida, gona, tallace-tallace, girmama na gaba.Matasa – aikin gayya, gida, niƙa 
6Tufafin Hausawa da kayan ado:  Ɗalibai su san Ire-iren tufafin Hausawa Hula: Dara, Zanna habal-kada, ƙube, malfa,                                   ɗankwara dsRiga: alkyabba. Kaftani, Jamfa, Jallabiya, malunmalun, Yar shara ds.Wando: Tsala, Kafi shanu, Buje, TureTakalma: Fed, kafi-katifa, gwandola ds. Shimi, ɗantofi, ɗanfatari, ɗankwali, gyale ds 
7Ci gaba da:     A tantace na sarauta: AlkyabbaRawaniKuftaAbayaShureYartofa dss 
8Auna fahimta:   Malami ya tabatar yara sun Kaifafa fahimtarsu game da labari ko waƙa.Da kuma su iya kawo ma’anar kalmomin Hausa 
9Malami ya kuma haƙiƙance cewa ɗalibai za su: Iya amsa tambayoyi na JawabiWaƙa A koyar da ma’anar auna fahimta da sigoginsa 
10Dabarun fassara:   A koyar da yadda ɗalibai za su: San ma’anar fassaraNaƙalci dabarun fassaraFassara ta’kaitattun bayanai ire-iren fassaraBaƙi da baƙiKalma da kalmaMai ‘yanci 
11Ci gaba da fassara:    A koyar da takaitacciyar fassara bayanai dangane da: ƘanjamauYoyon fitsariShan miyagun ƙwayoyiDangantakar maza da mata   
12MaimaitawaMaimaitawa
13JarabawaJarabawa

Share this Article
Leave a comment