Hausa Language Scheme of Work for JSS 3 Federal (All Terms)

7 Min Read
Schemeofwork.com
Scheme of Work

Nigerian Languages (NL), Federal Hausa language Scheme of work for JSS 3. Ma’ana da nau’o’in fassara Schemeofwork.com

HAUSA LANGUAGE L1 FIRST TERM SCHEME
ZANGO NA DAYA          AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1HARSHE: Garbatar da jimla mai harshen damo. Misalimyaron nana baki gare shi, ta ci wake, yaron ya koma. 
2HARSHE: Takaitaccen bayani akan lokutan Hausa. Misali – lokaci mai zuwa, lokacin yanzu da lokaci wanda ya gabata 
3ADABI: Nazarin saukakan rubutattun waƘoƘi masu ɗango biyu-biyu zuwa uku-uku. 
4ADABI: Gabatar da bayani akan rubtun zube. 
5AL’ADA: Ma’anar tsaro da nau’o’ina. Misali – tsaron kai, gida, gari, kasa ds. 
6AL’ADA: Ma’anar sana’a da ire-irenta. Misali – noma, Ƙiwo, rini, Ƙira, saƘa, dukanci, jima, ɗinki, gini, ds. 
7HARSHE: Amfani da baban baki ko karami a inda ya dace. 
8ADABI: Ci gaba da nazari akan zaɓaɓɓun rubutattaun waƘoƘi. (A kula da zubi da salonta tare da jigonta) 
9AL’ADA: Bayani akan hukumomin tsaro da irin ayyukansu. Misali- yau sauda, soja (sama, kasa, ruwa) kwastan, jamian kula da shiga da fice, yau saudan – ciki, da ganduroba. 
10AL’ADA: Tsokaci akan muhimmancin sana’a. misali – dogaro da kai, kare mitunci, samun abin masarufi, haɓaka tattalin arziki ds. 
11ADABI: Ci gaba da nazari akan rubutun zube , misali- kula da zubi da tsarin labari tare da jigonsa. 
12HARSHE: Haɗawa ko raba Ƙalmomi inda ya dace. Misali- kodayaushe, ci gaba, barkonon-tsohuwa, matsattsaku, shasshaka, ds. 
13Bitar aikin baya/maimaitawa   
14Jarabawa 

HAUSA LANGUAGE L1   SECOND TERM
ZANGO NA BIU             AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1HARSHE: Ma’ana da nau’o’in fassara. Misali – ta baki (tafinta), da ta rubutu. 
2ADABI: Nazari da bayanin zababbun rubutattun wasan ƘwaiƘwayo. 
3ADABI: Ma’anar adabin baka da rukunoninsa. Misali – waƘoƘin baƘa, tatsuniyoyi, labaran gargajiya, zaurance, Karin nagana, waƘoƘin makaɗa ds. 
4AL’ADA: Ma’anar kare-saye da haƘƘoƘin kare saye. (kiyaye haƘƘoin mai saye daga mai sayarwa). Misali – samum biyan buƘata, rashin illa ga lafiya, samum bayani, ds. 
5AL’ADA: Nazari akan hanyoyin haɓaka tattalin arziki na zamani. Misali – noma da kiwo na zamani, sarrafa kayan abinci. 
6HARSHE: Cikakke bayani akan rubutacciyar fassara. Misali – fassara mai yanci da mara yanci. 
7ADABI: Ci gaba da nazari akan rubutaccen wasan ƘwaiƘwayo. (kula da jigo da salon wasa) 
8ADABi: Ci gaba da bayani akan ruƘunonin adabin baƘa. 
9AL’ADA: Ci gaba da bayani kan haƘƘoƘin kare saye. Misali – haƘƘin zaɓi, kai kuka, ilimantar da kai, koke ds. 
10AL’ADA: Ci gaba da nazarin hanyoyin habaka tattalin arziki. Misali – sana’o’in hannu na zamani, da cinikayyar zamani 
11Bitar aikin baya/maimaitawa   
12Jarabawa 

Nigerian Languages (NL), Federal Hausa language Scheme of work for JSS 3. Schemeofwork.com

HAUSA LANGUAGE L1  THIRD TERM
ZANGO NA UKU           AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1ADABI: Ma’anar rubutaccen adabi da ruƘunoninsa 
2AL’ADA: Ma’anar da misalan keta haddi. Misali – satar mutane, safarar mutane, azabtar da yara da gallazawa mata. 
3HARSHE: Bayani kan auna fahimta da nau’o’in sa. Misali – na wayar da kai, fasaha da ƘirƘire-ƘirƘire. 
4ADABI: Ci gaba daa cikakken bayani akan rukunonin rubutaccen adabi. Misali – rubutun zube, rubutacciyar waƘa da wasan ƘwaiƘwayo. 
5HARSHE: Ci gaba da bayani akan auna fahimta. Misali –  fasahar Ƙwanfuta da sadarwa 
6AL’ADA: Illolin keta haddin al’umma. Misali – karuwanci, Ƙangarewa, shaye-shaye, hauka, ds. 
7Bitar aikin baya/maimaitawa   
8Jarabawa 

HAUSA LANGUAGE L2    FIRST TERM
ZANGO NA DAYA           AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1HARSHE: Ƙa’idojin rubutu misali-amfani da babban bakiko Ƙaramin baki inda ya dace.  
2HARSHE: Koyar da alamomin rubutu. Misali-aya, waƘafi, karan ɗori, alaman motsin rai, baƘa biyu ds 
3HARSHE: Koyar da kiɗaya daga 100-1000 
4HARSHE: Sunayen zahiri da badini misali-zafi, sanyi, iska, teburi, mota, kujera, d.s. 
5HARSHE: Ma’anar insha’i da rabe-rabensa (na labari, muhawara, bayani, rubutun wasiƘa.dis) 
6HARSHE: Sigar rubutun wasiƘa misali-adireshi, kwanun wata, gaugaur jiki. d.s. 
7HARSHE: Hadawa ko raba Ƙalmomi inda ya dace. 
8ADABI: Ma’anar Ƙarin magana da misalai. Misali-komai nisan jifa……..rabon Ƙwado…..d.s. 
9HARSHE: Tambaya da amsa, hira tsakanin aboki. 
10HARSHE: Koyar da rubutu da karatu a aji. 
11ADABI: Koyar da halin da mutum ke ciki misali-farin ciki, juyayi, bakin ciki (labarin zucuja a tambayi fuska) 
12HARSHE: Ma’anar ingausa tare da misali. Misali-zanje makaranta, ya tafi kasuwa d.s. 
13Bita/maimaita aikin baya 

HAUSA LANGUAGE L2  SECOND TERM
ZANGO NA BIU             AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1HARSHE: Ma’anar fassara da rabe-rabenta 
2HARSHE: Fassara Ƙalmomin turanci zuwa hausa. Misali-fassara Ƙananan jinloli da gajerun labarari. 
3ADABI: Wayar da kai game da ciwon sida (hiv),da shan miyagun kwayoyi. 
4HARSHE: Kara Ƙarfafa bayani kan auna fahimta 
5HARSHE: Koyar da Ƙalmomi tare da Ƙishiyoninsu.misali-rayuwa-mutuwa,zauna-tashi d.s. 
6AL’ADA: Abincin hausawa (ganyayen da hausawa keci) misali-zogale,rama,dinkin,kauci,yadiya,alayyahu d.s. 
7AL’ADA: Ma’anar sana’a da rabe-rabenta (ta mata da ta maza) 
8AL’ADA: Bayani kan sana’ar noma da kiwo 
9AL’ADA: Bayani a kan Ƙira da wanzanci 
10AL’ADA: Bayani kan sana’ar fawa da su.   
11Bita/maimaita aikin baya 
12Jarabawa. 

Nigerian Languages (NL), Federal Hausa language Scheme of work Schemeofwork.com

HAUSA LANGUAGE L2  THIRD TERM
ZANGO NA UKU           AJI UKU

MAKOBATU/KUMSHIYAAYYUKA
1ADABI: Manar rubutaccen adabi da ire-irensa misali-rubutun zube; wasan ƘwaiƘwayo, rubutattun waƘoƘi). 
2ADABI: Ci gaba da bayani adabi. 
3AL’ADA: Ma’anar maganin gargajiya da ire-irensa. misali-turare,shafi,sake-safi,sabara,dauri,d.s. 
4HARSHE: Fassara Ƙananan Ƙalmomi   
5Bitar aikin. zangon karatu na ɗaya da na biyu. 
6Bitar aikin zango karatu na uku. 

Share this Article
Leave a comment